Jami'in Dansanda ya harbe wani Matashi har lahira a Abuja
Wani jami'in Dan Sanda ya harbe wani Matashi mai suna Abba Dan asalin jihar Katsina wanda jami'an hukumar Æ´ansanda suka kama da laifin yin talla a kasuwar wuse dake cikin garin Abuja.
Matashin Wanda yayi niyar guduwa da ankwa a hannusa sai wannan Dan sandan ya harbeshi nan take rai yayi halinsa.
Shidai wannan matashi ba Dan ta'adda bane ba ba barawo bane ba laifin Abba shine yin talla a cikin garin Abuja bayan da hukuma ta hana talla a babban birnin tarayyar Najeriya din.
Abbah yayi niyar guduwa ne daga Hannun Jami'an sakamakon wannan bashi bane kamun da akai mashi na farko ba, Abbah bai dade da fitowa daga gidan yari ba wannan dalilin ne yasa yayi niyar guduwa ganin cewa yasha wahala a lokachin da aka kamashi a karo na farko, lokachin da Abbah yayi niyar guduwa ne wani jami'i ya harbeshi da bindiga inda a take Abbah yace ga garinku nan.
Zuwa yanzu Muryar Labarai Bata samu zantawa da hukumar yan sandan ba domin Jin wane mataki zata dauka.
0 Comments