Yawan wadanda aka kashe a harin Jihar Filato ya kai 113

Yawan wadanda aka kashe a harin Jihar Filato ya kai 113.

Adadin wadanda suka mutu a hare-haren da aka kai a karshen mako a jihar Filato da ke tsakiyar Najeriya ya karu zuwa 113, in ji wani jami'i a ranar Litinin, a yankin da ake yawan samun rikici tsakanin makiyaya da manoma.

Tun da fari kamfanin dillancin labarai na AFP ya rawaito rundunar sojin Najeriya a jiya Lahadi tana cewa mutum 16 ne suka mutu a sabbin hare-haren.

Wannan dai shi ne tashin hankali mafi muni da ya barke a Filato tun watan Mayu, lokacin da aka kashe fiye da mutum 100 a hare-haren manoma da makiyaya.

Tun da fari kamfanin dillancin labarai na AFP ya rawaito rundunar sojin Najeriya a jiya Lahadi tana cewa mutum 16 ne suka mutu a sabbin hare-haren.

Shugaban riƙo na karamar hukumar Bokkos a Jihar Filato, Monday Kassah, ya ce an kashe mutum 113 a hare-haren da aka kai a ranakun Asabar da Lahadi.

"Hare-haren sun kasance waɗanda aka tsara su sosai. Aƙalla al'ummomi daban-daban 20 ne 'yan bindiga suka kai wa hari," in ji shi.

"Mun gano gawarwakin mutum 113 daga cikin wadannan al'ummomi, mun kuma gano sama da mutum 300 da suka jikkata."

Kassah bai bayyana ko su wane ne ke da alhakin kai hare-haren ba. Ya kara da cewa an kai wadanda suka jikkata asibiti.

Jihar Filato dai na daya daga cikin jihohin da ke fama da rikicin bambancin Æ™abila da addini, inda irin waÉ—annan rikice-rikicen suka yi sanadin mutuwar É—aruruwan mutane a ‘yan shekarun nan.

Ana yawan kallon tashin hankalin a matsayin rikicin kabilanci da addini tsakanin makiyaya Musulmai da galibin manoman Kiristoci. Amma sauyin yanayi da faÉ—aÉ—ar aikin noma su ma manyan abubuwa ne da ke taka rawa wajen ta’azzarar rikicin.

Post a Comment

0 Comments