KAI-TSAYE: Sojojin Isra'ila sun sake kama Falasdinawa 40 a Yammacin Kogin Jordan
Hare-haren da Isra'ila ta kwashe kwana 55 tana kai wa Gaza sun yi sanadin mutuwar Falasdinawa akalla 16,000, galibinsu mata da kananan yara. Kimanin mutum 7,000 aka danne a baraguzan gine-gine wadanda Isra'ila ta yi wa luguden wuta, a cewar hukumomi.
Kungiyar ta FalasÉ—inu mai zaman kanta ta bayyana cewa kamen na baya-bayan nan ya sa yawan FalasÉ—inawan da aka tsare tun ranar 7 ga watan Oktoba ya kai 3,365.
— Sojojin Isra'ila sun sake kama Falasdinawa 40 a Yammacin Kogin Jordan
Rundunar sojin Isra'ila ta tsare aƙalla Falasɗinawa 40 a wani samame da ta kai Yammacin Kogin Jordan da safiyar ranar Alhamis, a cewar Ƙungiyar Fursunoni ta Falasɗinawa.
Kungiyar ta FalasÉ—inu mai zaman kanta ta bayyana cewa kamen na baya-bayan nan ya sa yawan FalasÉ—inawan da aka tsare tun ranar 7 ga watan Oktoba ya kai 3,365.
Tashin hankali na ƙaruwa a Yammacin Kogin Jordan a yayin da sojojin Isra'ila ke kai hare-hare Zirin Gaza tun bayan harin ba-zatan da Hamas ta kai wa Isra'ila ranar 7 ga watan Oktoba.
An kashe mutum uku a harin da aka kai a Gabashin Birnin Ƙudus
Aƙalla mutum uku ne suka mutu sannan shida suka jikkata, ciki har da biyun da ke cikin wani mummunan yanayi, a wani harbe-harbe da aka yi a yankin Gabashin Birnin Kudus da Yahudawa ƴan kama wuri zauna suka mamaye.
'Yan sanda sun ce a ranar Alhamis din nan an kashe mutum biyu da ake zargi da hannu a harbe-harben a nan take bayan harin da aka kai a kusa da tashar motar bas da ke Yammacin Birnin Kudus, inda babu shingayen binciken ababen hawa da ke gadin hanyar shiga birnin.
‘Yan ta’adda biyu ne suka isa a mota, daya daga cikinsu dauke da M-16, É—aya kuma É—auke da bindiga,” inda suka buÉ—e wuta, kamar yadda shugaban ‘yan sandan Kudus, Doron Torgeman ya shaida wa manema labarai a wurin.
Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Magen David Adom ta ce daya daga cikin waÉ—anda abin ya shafa wata mace ce mai shekara 24 da haihuwa.
Harin na zuwa ne jim kadan bayan da aka tsawaita wa'adin tsagaita wuta a Zirin Gaza tsakanin mayaƙan Falasdinawa da Isra'ila na tsawon kwanaki bakwai, kafin cikar wa'adin.
0 Comments