"Duk lokacin da na duba wayarsa, nakan ga wani abu da ke fusata ni. Da alama yakan yi hira da wasu matan," in ji Rabi.
A ko yaushe Rabi kan ƙagu ta ga ya ajiye wayarsa akan tebur don shiga wanka, inda ita kuma sai ta lallaɓa ta ɗauki wayar .
Daga Abdulwasiu Hassan
Wayar hannu da ke haɗa zumunci a tsakanin miliyoyin zukata a cikin ƙasa mafi yawan al'umma a Afirka, a yau kuma tana zama sanadin rusa zamantakewa.
Wasan kyanwa da É“era ake yi a kowane yammaci tsakanin Isa (ba sunasa na gaskiya ba) da matarsa a kan batun waya. Rabi (ba sunanta na gaskiya ba) ta tsiri al'adar son duba wayar mijinta a duk lokacin da ya dawo daga aiki.
A koyaushe takan ƙagu ta ga ya ajiye wayarsa a kan tebur don shiga wanka, ita kuma sai ta lallaɓa ta ɗauki wayar.
Kamar yadda ta saba, Rabi cikin gaggawa takan fara binciken wayar don ganin waɗanda suka kira shi da kuma saƙonninsa. Sau da dama hakan kan saka ta a cikin damuwa maimakon kwanciyar hankali.
Duk lokacin da na duba wayarsa, nakan ga wani abu da kan fusata ni. Da alama yana yawan hira da wasu matan," ta faÉ—a cike da jin takaici.
Yadda waya ke jawo matsala
Ba Rabi ce kadai ke da irin wannan halayya ba. A Nijeriya, wayar tafi-da-gidanka tana haifar da rashin jituwa tsakanin ma'aurata da dama, tana haifar da rashin yarda da kuma sanya shakku a cikin aure da dama.
Masaniyar ilimin halayyar ɗan'adam Aisha Bubah ta shawarci irin wadannan ma'aurata da su riƙa tattaunawa ta gaskiya a kan abubuwan da suke so da waɗanda ba so abokan zamansu su rika yi kafin a yi aure.
"Idan ba haka ba, za mu samu kanmu a yanayin da miji ko mata suke jin cewa É—ayan yana É“oye abubuwa a wayarsa, kuma hakan zai iya yin barazana ga dangantakarsu,”
Mata da dama na ganin ya zama wajibi su dinga duba wayoyin mazajensu.
"Sirrin kiyaye daidaito da tabbatuwar aurenku cikin zama lafiyashi ne a guji yin duk wani abu da ka iya zama barazana ga zamantakewarku.
Idan har kuna barin wasu shaidu ko alamu da abokin zamanka ba ya so a kan wayarka, to hakan zai iya haifar da matsala,” in ji masaniyar halayyar É—an'adam din da ke Abuja.
Matsalar da ta zama ruwan dare
Ko da yake za a iya ganin kamar ƙaramin abu ne, wannan rashin yarda da junan ya jawo har sai da wani tsohon gwamnan Jihar Kano kuma dan takarar shugaban kasa a Nijeriyar ya taɓa ba da misali da matsalar.
Ya shaida wa ma’aurata a wajen auren gata da gwamnatin jihar ta yi wa mutum 1,800 kwanan nan cewa, “Ina da shawara guda daya a gare ku: Ka da ku dinga binciken wayar abokan zamanku, saboda hakan na daga cikin manyan dalilin da ke jawo mutuwar aure a zamanin nan.
Mutane da yawa a Nijeriya sun yi imanin cewa yawan duba wayar abokin zama yana shafar zaman aure sosai. Amma akwai mutane irin su Rabi da suke ganin ya zama wajibi su dinga binciken wayar mijinsu don sanin me yake ciki.
Waya wata hanya ce ta bin diddigi. "Ya wajaba a kaina na gano dalilin da ya sa yake yawan shafe lokaci yana amfani da waya. Yana yawan sauya lambar sirri ta buuÉ—e wayar tasa, amma ko yaushe ya sauya sai na gano sabuwar,"
0 Comments