Ya kamata kowa ya san wannan!👇
Ƙasar JERŪSALEM ƙasa ce mai albarka wadda Allah da kansa ya tsarkake.
Ita ce ƙasar da Allah ya ambata a cikin Al-ƙur'ani.
Ita ce ƙasar da aka gina Masallaci na biyu a doron ƙasa.
Masallacin QUDUS shine Masallacin da Sallah É—aya take daidai da Salloli 250.
Wanna ita ce ƙasar da aka ɗauki Manzon Allah ﷺ daga cikinta zuwa sammai domin saduwa da Allah.
Ita ce ƙasar da Manzon Allah ﷺ ya jagoranci dukkan Annabawa Sallah a cikinta.
Ita ce ƙasar da aka fuskanta a cikin Sallah wata goma 16 kafin a juya zuwa fuskantar Ka'aba 🕋
Ita ce ƙasar da Mala'ikun Allah suke shimfiɗa fikafikansu a kanta har zuwa yau.
Ita ce ƙasar da Manzon Allah ﷺ ya ɗauki kofin nono ya sha, sakamakon haka aka shiryar da al'ummarsa zuwa ga tafarki madaidaici. Idan da ya ɗauki kofin giya da dukkan al'ummarsa na kan ɓata.
Ita ce qasar da Annabi Isa عليه السلام zai kashe babbar fitina a doron ƙasa, (watau Dajaal).
Ita ce qasar da Annabi ﷺ ya ce: mafifitan Mutanen Duniya za su zauna a cikinta, itace ƙasar da Annabi Ibrahim عليه السلام ya yi hijira (watau Jerūsalem).
Ita ce ƙasar da Annabi Musa عليه السلام ya roƙi Allah ya bar shi ya mutu a kusa da ita.
Duk Musulmi na neman kusanci ga Allah da son wannan ƙasar.
Ha'intar wannan ƙasar, cin amanar Allah ne da Manzon Allah ﷺ, kuma haramun ne ga mumini ya ci amanar Allah da Manzonsa.
To yanzu ka sanar dani, ta yaya maƙiya Allah zasu ɗauka cewa Musulmi zasu bari a taɓa wannan ƙasar???
A duk lokacin da muminai suka ce za su mutu suna kare wannan ƙasar, a haƙiƙa suna nufin kare ta ne saboda waɗannan dalilai.
Ya ubangiji Allah ka taimaki Addinin Musulunci da Musulmi! Allahumma Ameen 🤲
0 Comments